An kada kuri'ar zaben shugaban kasa a Guinea

Taswirar Guinea
Image caption Soji suna shirin yin bankwana da mulki

Mutane na ta farin ciki a kasar Guinea da ke yankin yammacin Afrika, inda masu zabe suka kada kuri'a a wani abinda zai iya zama sahihin zabe na farko tun samun yancin kai, shekaru 52 baya.

Soji da a halin yanzu ke rike da iko sun hana sojoji tsayawa takara a zaben.

Dubun-dubatar ‘yan kasar ta Guinea ne ke kada kuri'a a ko'ina cikin kasar.

Daya daga cikin ‘yan takarar shugabancin kasar, Sidya Toure, ya ce ga galibin mutane a kasar, samun abin rayuwar yau da kullum, ya fi damokuradiya muhimmanci.

Ya ce, ba demokuradiya ne abu na farko da mutane ke tambayarka ba.

Suna magana ne a kan abinda za su ci, da muhalli da samar da rowan sha.

Kasar ta Guinea dai ta auka cikin yamutsi a watan Satumba bayan da dakaru suka bude wuta a kan masu zanga zangar neman damokuradiya, inda suka kashe mutane fiye da 150.