'Yan adawa a Najeriya za su tsaida dan takara guda

Taswirar Najeriya
Image caption Ko kai zai hadu kuwa har zuwa zabe?

A Nigeria, wasu jam’iyyun siyasa a kasar sun bayyana aniyarsu ta hada kai domin tsayar da dan takarar shugabancin kasar guda daya tilo.

Jam’iyyun sun kuma bayyana cewa lokaci na neman kure wa hukumar zabe ta kasar, ganin cewa har yanzu akwai wasu muhimman abubuwan zaben da ba a yi su ba.

Sun hada da gyaran dokokin zabe, da tsayar da lokacin zaben da ma rajistar masu zaben.

Sai dai wasu na ganin da wuya wannan aniya ta jama'iyyun ta kai gaci, saboda a baya an sha shirya irin wannan gamayya, domin kalubalantar jam’iyyar PDP mai mulki, amma kuma sai maganar ta lalace.