Fafaroma ya koka a kan binciken lalata a coci

Fafaroma
Image caption 'Yansanda sun ce su bi ka'ida wajen kai samamensu.

Fafaroma Benedict ya tsoma baki kai tsaye a wata takaddama game da samamen da ‘yansanda suka kai a coci-cocin Roman Katolika a Belgium ranar Alhamis.

Samamen dai wani bangare ne na bicike kan lalata da kananan yara da ake zargin malaman Cocin ta Katolika.

Fafaroman ya kira halayyar ‘yansandan da cewa abin kyama ne, ya kuma ce dole ne a mutunta yancin cocin.

Fadar Fafaroma ta Vatican ta zargi ‘yansanda da tsare wani gungun bishop-bishop a cikin wani coci har tsawon sa’a 9.

Sai dai Ministan Shari’a na Belgium ya ce, an bi tsarin aikin yansanda yadda ya kamata, kuma an baiwa jami'an cocin damar samun abinci da abun sha.

Wakilin BBC ya ce, a cikin watan Afrilu wani jami'in coci ya yi murabus bayan da ya zama na farko da ya amsa cewa ya yi lalata da yara yayin da yake Bishoop, kuma tun daga nan an samu daruruwan rahotannin cewa jami'an cocin sun yi ta lalatar da kananan yara.