Za a iya soma tattaunawa da Taleban

Janar Sir David Richards
Image caption Ko yakin Afghanistan ya kusan zuwa karshe ke nan?

Shugaban sojin Birtaniya, Janar ya ce za a iya soma yin tattaunawa ba da jimawa ba tare da kungiyar Taleban a Afghanistan.

Janar Richards ya sheda wa BBC cewa wannan ra'ayin kashin kansa ne, amma babu wani dalili da zai hana a duba yiwuwar yin shawarwari.

Ya ce idan har za a soma sasantawa, wata kila ta kasance da farko ta hannun wani mai shiga tsakani.

Ya ce amma a lokaci guda, dole mu ci gaba da abinda muke yi ta fuskar soji, da shugabanci da raya kasa domin kada su dauka cewa mun mika wuya gare su.

Yan kwanakin da suka wuce ne dai Piryim Ministan Birtaniya David Cameron ya ce yana son dakarun Birtaniya su bar Afghanistan cikin shekaru 5.