Hukunci kan mallakar bindigogi a Amurka

kotun kolin Amurka
Image caption Kotun kolin Amurka ta ce 'yancin Amurkawa ne su mallaki bindigogi, domin kare kai.

Kotun kolin Amurka ta yanke hukuncin cewa babu wani birni, ko gwamnatin wata jiha da zata haramta wa Amurkawa mallakar bindigogi.

A wani hukunci da alkalai biyar suka amince, hudu suka nuna adawa, kotun ta ce sashen tsarin mulki da ya bai wa dan kasa 'yancin mallakar bindiga domin kare kai, na aiki a duk fadin kasar.

A sakamakon wannan hukunci, matakin da jihar Chicago ta dauka na haramta mallakar bindiga ya saba ma kundin tsarin mulki.

Babu tabbas kan tasirin da hukuncin zai yi a sauran fannoni, amma kotun ta ce, ba tana so ne ta haramta matakan sa ido ba.