Hadarin mahakar ma'aidinai a Ghana

A kasar Ghana rahotannin dake fitowa daga garin Dunkwa-on-Offin dake jihar tsakiyar kasar sun ce akalla wasu masu hakar zinariya ba bisa ka'ida ba su 35 ne ake kyautata zaton cewa sun hallaka, bayan da wani rami da suke hakar zinariyar a cikinsa ya rufta a kansu a jiya.

Masu hakar zinariya wadanda aka fi sani da sunan galamsey sama da dari(100) ne dai aka kiyasta cewa suna cikin ramin a lokacin da hadarin ya auku, to amma wasu daga cikinsu sun tsira da rayukansu.

Ramin da suke hako ma'adanan ne dai ya rufta, sakamakon ambaliyar ruwa da ya kwarara zuwa ramin daga kogin Offin a garin Dunkwa.

Ana kyautata cewa da dama daga cikinsu dai sun mutu ne , saboda jinkirin da aka samu wajen kai musu dauki.