Jinkirin ruwan sama a wasu sassan jamhuriyar Niger

Taswirar Niger
Image caption Taswirar Niger

A jamhuriyar Niger, hankalin manoma ya fara tashi a wasu yankunan kasar, saboda jinkirin da aka samu wajen saukar damina a yankunan nasu.

Daya daga cikin matsalolin da wasu manoman suka fara fuskanta tun farkon daminar sun hada da mutuwar shuka, yayin da guzurin wasu manoman ya yanke gabanin saukar daminar.

Sai dai hukumar bincike da hasashen yanayi ta kasa ta yi kira ga manoman da su kwantar da hankalin su a game da damina mai zuwa.

A wannan shekarar kimanin mutane miliyan 7 ne suke fuskantar matsalar karancin abinci, sakamakon rashin isasshen ruwan sama a bara.