Yan Rwanda na dari-darin komawa gida

Rwanda
Image caption Kawunan mutanen da aka kashe a Rwanda

Yan gudun hijira kasar Rwanda

Wani rahoto ya ce shekaru goma sha shida bayan kisan kare dangin da ya faru a kasar Rwanda, dubunnan yan gudun hijira daga kasar na darin -darin komawa gida.

Wadanda suka wallafa rahoton sun ce duk da matsin lambar da hukumar kula da yan gudun hijira ta Majilisar Dinkin Duniya da kuma hukomoin Rwanda keyi , kawo yanzu yan gudun hijira sun ki barin kasar Uganda .

Wani dan gudun hijira ya fada wa masu gudunar da bincike, daga kungiyar kare hakkin yan gudun hijira, ta kasashen waje a Uganda cewa komawa Rwanda kamar mutum ya sa hanunsa ne a cikin ramin maciji.

Wakilin BBC ya ce yan kabilar Hutus, sune yan gudun hijira da su ki koma gida kuma ana zargin su da aiwatar da kisan kare dangi, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutune dubu dari takwas wadanda galibin su yan kabilar Tutsi ne.

Yan gudun hijirar dai sunyi amanar cewa Gwamnatin Rwanda zata nuna masu banbanci idan sun koma gida .