Turkiya ta hana jiragen yakin Israila shiga sararin samaniyar ta

Praministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan
Image caption Praministan Turkiya Recep Tayyip Erdogan

Praministan Turkiya, Recep Tayyip Erdogan, ya ce gwamnatinsa ta daina barin jiragen yakin Israila su yi amfani da sararin samaniyar kasar.

Mr Erdogan ya bada sanarwar ce, bayan da Turkiyar ta tilastawa wani jirgin sojan Isra'ila dauke da hafsoshin soja zuwa Poland, bin wata hanya mai nisa don kaucewa sararin samaniyar Turkiyar.

Jami'an gwamnatin Turkiya dai sun ce haramcin ba zai shafi jiragen sama na daukar pasinja ba.

Dangantaka na kara yin tsami tsakanin Isra'ila da Turkiya, tun bayan kisan wasu mutane 9 'yan Turkiyar, wadanda ke cikin wasu jiragen ruwa da suka yi kokarin kai agaji zuwa Gaza a watan jiya.