Congo na bukin cika shekaru hamsin

Congo
Image caption Papa Wemba shahareren mawakin kasar congo

Jamhuriyar Congo ta cika shekaru hamsin da samun yancin kai

A yau ne Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo , ke bikin cikarta shekaru hamsin da samun yancin kai, daga mulkin mallakar Belgium, inda ta ke fatan kyautata sunanta bayan yaki, da talauci da almundahana su ka yi mata kaka-gida.

An dai yiwa Kinshasa babban birnin kasar, gyaran fuska domin tarbar manyan bakin da suka hada da sakatare janar na MDD, Ban ki-moon, da sarkin Belgium Albert na biyu.

Sai dai al'umar Congo da dama ba za su yi wata murna ba, kasancewar suna rayuwa ne cikin kangin talauci duk da arzikin ma'adinan da kasar ke da shi.

Wakilin BBC ya ce a yanzu kasar Congo na fama da tsanananin talauci da kuma yawan rikice-rikice.

Iya kwalliya da kuma kidan da ke burge duniya ne kawai abinda kasar za ta iya tinkaho da su.