Fari a Nijar ya jefa rayuwar Buzaye cikin hadari

Rayuwar Buzaye a Nijar
Image caption Shugaban wata tawagar Buzaye a Nijar,Youseff al-Hamada

Duk da irin ci gaban da duniya ke fuskanta, al'umar Buzaye sun kasance suna rayuwa a cikin hamadar Sahara tare da dabbobin su, sai dai yanzu illar da fari ya haifar ga miliyoyin 'yan Nijar ya fara shafar Buzayen. Ganin yadda ake fama da karancin ruwa da mutuwar dabbobi, da dama daga cikin Buzaye sun fara kaura daga dazuka zuwa birane.

Buzayen sun kafa tantuna na tsaffin buhuna da robobi da kuma shara a wajen birnin Yamai, inda kimanin Buzaye 17 da suka yo kaura daga dazuka ke zaune.

Kuma a cewar shugaban su Youseff al-Hamada, farin da ake fama da shi a kasar ya sa ba za su iya zama a dazukan ba, domin wurin ya fi karfin rayuwar bil'adama. Wadannan Buzaye sun samu kan su a wurin da ke da nisa sosai da inda suka saba rayuwa.

"Sannu a sannu rayuwa na kara tsauri a sahara, sannan rashin tabbas na ta karuwa," a cewar Youseff. "Hakan ya sauya yadda jama'ar mu ke rayuwa. A daidai lokacin da kuma gudun hijira ke karuwa. Dabbobi da dama na mutuwa, abinda yasa muke fuskantar karancin nama da madara. Abin da kuma ya sa muka kasa ci gaba da rayuwa."

Image caption El Kassim daya daga cikin 'ya'yan Youseff, yana kwance a wani tanti

Yace idan har ba a samu damuna mai kyau ba, to ba za su iya komawa domin ci gaba da rayuwa a Sahara ba.

A cewar sa wannan matsalar, da kuma nauyin da ya ke kan sa na ciyar da yara bakwai ciki har da biyar na dan-uwansa wanda ya rasu, ya tilas ta masa kaura zuwa babban birnin Yamai.

Yayin da shi da jama'arsa suka isa birnin, sun yi mamakin abin da suka gani. "Ban san kowa ba, babu mai jin yare na kuma ban saba ganin jama'a da yawa haka a wuri guda ba."

Ya kara da cewa: "Mun saba rayuwa mu kadai. Amma akwai kazanta a nan, jama'a na zubar da shara ko'ina. Mun saba da rayuwa kan duwatsu da iska mai ban ni'ima."

Zargin aikata laifuka

Mazauna birnin Yamai da dama ne ke zargin Buzaye da laifin aikata fashi da makami da safarar miyagun kwayoyi da tayar da hankula, da kuma alakanta su da kungiyar al-Qaeda.

Kuma Youseff ya amince cewa wasu daga cikin mutanen su kan yi rikici a lokuta da dama, sai dai yace sukan yi fada ne kawai idan akwai dalilin yin hakan. Amma ya musanta cewa jama'ar su nada lalaci, yana mai cewa rashin ilimi da gogewa ne yasa ba sa yin aiki.

Ya kara da cewa rayuwa na da wahala cikin birni, kuma yana fuskantar matsi wajen samun abin da zai ciyar da iyalin sa.

Sannan yace akwai yiwuwar al'umar Buzayen su rasa al'adun su na gargajiya da suka gada daga iyaye da kakanni.

"Idan aka ci gaba da fuskantar fari, to rayuwar mu za ta sauya, inda za mu ci gaba da zama a birni, sai dai za mu rasa harshen mu da al'adun mu".

Sabanin ra'ayi

Amma duk da wannan wahala, dan Youseff, El Kassim, yana so ya ci gaba da zama a cikin birni.

Sai dai El-kasim, dan shekaru 13, ba shi da ra'ayin mahaifin nasa, domin cewa yayi: " Akwai duk abin da muke bukata a nan".

"Akwai makarantu, akwai asibitoci, wadanda babu makamantan su a sahara."

Youseff ya kara da cewa irin wannan ra'ayi na El-kasim, "ka iya sa jama'ar mu yin kaura kwata-kwata daga sahara zuwa birane". Kuma yana nuna irin yadda salon rayuwar Buzaye ta asali ke zuwa karshe.