Ma'aikatan bankuna suna yajin aiki a Nijer

Nijer
Image caption Nijer

A jamhuriyar Niger, hadaddiyar kungiyar ma'aikatan bankuna mai suna SYNBANK ta fara wani yajin aiki na tsawon kwanaki biyu kama daga yau.

Wannan yajin aiki dai ya jefa da dama daga cikin masu ajiyar kudi a bankunan a cikin wani mawuyacin hali.

Ma'aikatan bankunan dai na bukatar shugabbannin bankunan kasar da su kyautata makomar su ta hanyar yi musu karin alawus- alawus, musamman ma bayan sun yi ritaya.

Sai dai a bangaren kungiyar Shugabbannin bankunan ta AP-BEF, wannan bukata ta yan kwadogon ba za ta samu karbuwa ba.