Rasha ta yi watsi da zargin Amurka kan leken asiri

Gidan da aka kama wadanda ake zargi
Image caption Gidan da aka kama wadanda ake zargi

Kasar Rasha tayi watsi da batun kama wasu 'yan kasar ta da ake zargi da leken asiri a Amurka fiye da shekara goma da suka wuce da cewa batu ne mara tushe, kuma ikirari ne da Amurka ke yi da bai dace ba.

Sergei Lavrov shi ne ministan harkokin wajen Rasha kuma yace ba suyi bayani game da batun ba.

Wani kakakin ma'aikatar harkokin wajen Rashan yace zargin tamkar wani tuni ne na yakin cacar baki tsakanin kasashen biyu, kuma abin takaici ne da yazo a daidai lokacin da gwamnatin Obama ke cewa tana neman gyara dangantaka tsakaninta da Rasha.

Amruka dai ta cafke mutane goma da ake zargin 'yan leken asirin Rasha ne, yayinda mutum na goma sha dayan kuma ke tsare a Cyprus.