An ce matakan ceto kogin Kwara na aiki.

A jamhuriyar Nijar kungiyar kasashe masu amfani da ruwan kogin kwara ko Isa, ABN , ta ce ta cimma nasarori da dama dangane da kokarin da take yi na ceto kogin daga wadansu matsaloli da ke hana ruwan kogin malala yadda ya kamata.

Kungiyar ta ce a shekara mai zuwa ne za a fara ayyukan ginin dam din nan na Kandaji da ke Nijar, tare da gudanar da wasu ayyukan gyare gyaren dam din Kainji na Najeriya , don taimakawa wajen samar da isasshen karfin wutar lantarki.

Shugabannin kungiyar ta ABN ne suka tabbatar da haka yau din nan a birnin Yamai yayin wani taron manema labarai bayan sun shirya ma 'yan jaridan wata ziyarar gani da ido na ayyukan da kungiyar ke yi don kare kogin.