Almundahana a kasuwar zuba jarin Najeriya

Nigeria
Image caption Kudin Najeriya

Almundahana a kasuwar zuba jarin Najeriya

Hukumar kula da hadar hadar hannayen jari a Najeriya, ta ce zata binciki cibiyoyin kasuwancin da kuma wasu mutane da kuma kamfanonin da ake ganin cewa suna da hanu, a badakalar bankunan kasar .

Ta ce bayanai na nuna cewa ,akwai wasu jamian kasuwar hada hadar hannayen jarin kasar , da kuma kamfonin kudi da aka yi amfani da su wajen gudunar da zamba.

Shugbar Hukumar Arunma Oteh, ta ce zata tuhumi duk wanda ake zargin da sabawa kai'dar hadar- hadar kudin kasar.

Ta kuma ce zata gurfanar da kamfanin dari biyu, da kuma mutanen da ake zargin cewa suna da hanu a cikin wanan lamari.

Madam Arunma ta kuma ce tana son a tilsata musu biyan haramtaciyyar ribar, da su ka samu domin biyan masu zuba jari.

Shugabar ta kuma ce tana da aniyar bayyana sunayen jami'an kasuwar hadar hadar hannayen jarin kasar domin hana su sake gudunar da kasuwanci a kasar kuma.