Kasuwanci tsakanin China da Taiwan ya bunkasa

Image caption Wakilan kasashen China da kuma Taiwan

Kasuwanci tsakanin China da Taiwan

A yau jami'an kasashen China da kuma na Taiwan zasu sa hanu kan wata yarjejeniya wadda zata bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen biyu.

Sai dai wasu na ganin cewa Kasar Taiwan itace zata fi amfana, da wanan yarjejeniya.

Ammah kuma China ta ce, ta hakura da ribar da ya kamata a ce ta samu karkashin yarjejeniyar saboda alummar Taiwan yanwanta ne.

Sai dai kuma masu adawa da wanan shirin a kasar ta Taiwan, na ganin hakan alama ce dake nuni da cewa Chinar zata yi amfani da wanan dama wajen samun goyon bayan jama'ar kasar ta fanin siyasa domin cimma burinta a kasar.