An kama yan leken asirin Rasha a Amurka

Image caption Jakadan Amurka a kasar Rasha

An kama yan leken asirin Rasha a Amurka

Ma'aikatar sharia'ar Amurka ta ce a an capke mutum goma bisa zargin yan leken asirin Rasha ne.

Ta ce a ranar lahadi din data gabata ne, aka kama mutanen ammah zakara ya ba na sha dayansu sa'a.

Hukomomin kasar sun ce wasu daga cikin su, sun tare a Amurka ne tun farkon shekarun 1990.

Ana dai zargin cewa daya daga cikin su ya gana da wani ma'aikacin Gwamnatin kasar, inda sukayi magana kan batun makamin nukliya.

Lamarin dai ya auke ne a dai dai lokacin da Shugaba Obama, ke kokarin inganta huldar dake tsakanin kasashen biyu.