An amince da dokoki kan kudaden garabasa ga ma'aikatan bankuna

Stephen Green Shugaban Bankin HSBC
Image caption Stephen Green Shugaban Bankin HSBC

Bayan kwashe watanni ana tattaunawa, gwamnatocin dake karkashin kungiyar tarayyar Turai da malisar tarayyar Turan sun amince da wasu sabbin dokoki kan yadda ake bada kudaden bonus ga bankuna.

Wanna dai shine karo na farko da aka amince kan kayyade kudaden bonus da ma'aikatan banki ke karba, tun bayan matsin tattalin arzikin duniya.

A cewar 'yan siyasa, suna son ma'aikatan bankunan su rika tunani sosai, kamin su yi irin kasadar da ta janyo matsalar kudade a duniya.

Nan da farkon shekara mai zuwa ce ake sa ran za a amince da sabbin dokokin.