Congo Kinshasa ta cika shekaru hamsin

Jamhuriyar dimokradiyyar Congo na bikin cikin shekaru hamsin da samun 'yancin kai daga mulkin mallaka da kasar Belgium ta yi ma ta.

Sojoji sun gudanmar da wani kasaitaccen parati, a Kinshasa, babban birnin kasar.

An dai kawata birnin, kuma cikin manyan bakin da suka samu halartar bikin sun hada da sakatare janar na majlisar dinkin duniya Ban ki- Moon da Sarki Albert na biyu na kasar Belguim.

Sai dai ga yawancin 'yan kasar dake rayuwa a kasa da dalar Amurka biyu a rana, bayan shekarun da aka shafe ana yaki, da kuma matsalar cin hanci da rashawa, bikin na yau ba shi da wani tasiri.