An yi jana'izar yaran da daki ya rufta mawa a Kebbi

Taswirar Najeriya
Image caption Taswirar Najeriya

An yi jana'izar wasu yara su goma sha hudu da suka rasa rayukansu, bayanda dakin da suke kwana a ciki ya rufta a kansu a garin Gwandu na jihar Kebbi ta Najeriya.

Yaran sun rasu ne sakamakon wani ruwan sama da aka yi a daren ranar talata.

Biyar daga cikinsu yan gida daya ne.

Yaro daya ne dai ya tsira da ransa daga cikin yaran sha biyar dake kwance a dakin.

Rundunar yansanda ta jihar Kebbi ta tabbatar da aukuwar lamarin.