Shugaban Najeriya ya shiga Facebook

Shugaba Goodluck Jonathan
Image caption Shugaba Goodluck Jonathan ya ce ya shiga Facebook ne don ganawa da 'yan Najeriya

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya shiga sahun miliyoyin jama'a a duniya wadanda ke amfani da shafin sada zumunta na intanet, wato Facebook.

Shugaban ya ce ya yi hakan ne domin cika alkawarin da ya yi na fadada alakarsa da mutanen Najeriya wadanda ke zaune a ciki da kuma wajen kasar.

A jawabin da ya wallafa a shafin nasa, Shugaban na Najeriya ya ce “Allah ya horewa Najeriya da jama’arta dimbin albarkatu; don haka na ke son ‘yan Najeriya su ba ni damar tattaunawa da su ta wannan hanyar domin ciyar da kasar gaba”.

Jim kadan bayan shigar ta sa ne dubban 'yan kasar suka fara aika masa da sakonnin neman kulla kawance da shi.

Abin jira a gani dai shi ne ko wannan matakin da shugaban ya dauka zai yi wani tasiri na a-zo-a-gani wajen sauya akalar al’amuran gwamnati a Najeriya.