Majalisar Wakilan Najeriya zata takaita jam'iyyu

Kakakin Majalisar wakilan Najeriya, Dimeji Bankole
Image caption 'Yan majalisar sun bayar da shawarar kar a yiwa jam'iyya rajista sai tana da ifishi a kashi biyu bisa uku na jihohin kasar

Wani kwamitin Majalisar Wakilan Najeriya na musamman ya kammala aikin gyaran wadansu dokokin da suka shafi zabe.

Jiya ne dai Majalisar ta karbi shawarwarin kwamitin wanda aka dorawa alhakin yin wasu gyare gyare da suka danganci yiwa jam'iyyun siyasar kasar rajista.

Majalisar wakilan ta kuma kada kuri'ar amincewa da shawarwarin da kwamitin ya gabatar mata.

Shugaban kwamitin, Hon. Mohammed Ali Ndume, ya shaidawa BBC cewa kwamitin nasu ya gabatar da shawarwarin da suka hada da cewa duk jam’iyyar da ba ta da ofishi a kashi biyu bisa uku na jihohin Najeriya da ma kashi biyu bisa uku na kananan hukumomi dari bakwai da saba’in da hudu, ba za a yi mata rajista ba.

Sannan kuma, a cewarsa, duk wata jam’iyyar da ta ke son rajista to wajibi ta kasance tana da mambobi akalla dubu goma a kowacce jiha, a kashi biyu bisa ukun jihohin kasar.

“Sannan [kuma] idan jam’iyya ba ta ci kujera daya a majalisar jiha ko ta kasa ba, to ba jam’iyya ba ce”, inji Hon. Ndume.

Batun rajistar jam'iyyun siyasa dai ya jima yana sanyawa ana kai ruwa rana a fagen siyasar Najeriya.