Mista Netanyahu ya yi tayin musayar fursunoni

Benjamin Netanyahu
Image caption Bukatar Hamas ta sha bamban

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce a shirye yake ya saki fursunonin Palesdinawa dubu 1, idan kungiyar Hamas za ta saki sojin nan Isra'ila da ta kama, Gilad Shalit.

A wani jawabi da ya yiwa al'ummar kasar kai tsaye, Mr Netenyahu ya ce a shirya Isra'ila take ta yi sassauci mai girma, amma ba mai sharaddi ba don ceto Saje Shalit.

Saje Shalit ya shafe shekaru fiye da 4 ana tsare da shi a zirin Gaza.

Sai dai wani kakakin kungiyar Hamas, Ayman Taha ya yi watsi da tayin Mr Netenyahu

Ya ce: Matslar, ba yawan fursunonin da zaa saki ba ne.

Matsalar ita ce ta sunayen wadanda Netenyahu ya ki ya sake su da kuma umarninm da ya bayar na hana fursunonin komawa gidajensu.

Iyalan Shalit din dai da wasu magoya bayansa fiye da dubu 1 sun cigaba da macin da suke yi zuwa birnin Kudis a wani bangare na kamfe din da suke na ganin an sako shi.