Magoya bayan Najeriya sun koka kan dakatar da Super Eagles

'yan wasan Najeriya
Image caption Najeriya ce tazo ta karshe a rukunin B da maki daya kacal

Shugaban kungiyar magoya bayan Super Eagles Otunba Yisa Olatunde, ya ce matakin da shugaba Jonathan ya dauka na dakatar da kungiyar kwallon kafa ta kasar, ya yi tsauri, kuma ba zai taimakawa kasar ba. Sai dai tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta kasar Alhaji Ibrahim Galadima ya gayawa BBC cewa matakin ka iya yin tasiri. A yanzu dai Najeriya na fuskantar fushin hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.

Hukumar dai ta dade tana adawa da duk wani tsoma bakin 'yan siyasa a cikin harkokin kwallon kafa na kasashe.

'Rashin tabbas'

A ranar Laraba ne hukumar kwallon kafa ta kasa NFF, ta nemi afuwar masoya kwallon kafa na kasar, sakamakon mummunar rawar da kasar ta taka a gasar cin kofin duniya.

"Babu wasu shugabanni da suka taba kai kasar zuwa dukkanin gasar kasa-da-kasa," hukumar ta NFF tace tana son kociya Lars Lagerbeck ya ci gaba da jagorantar kungiyar.

Wakilin BBC na fannin wasanni Piers Edwards, wasu ka iya fassara hakan a matsayin wani yunkuri na gwamnati domin mayar da shugabannin hukumar NFF saniyar ware.

Tun da farko mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan al'amuran yada labarai, ya ce shugaban ya nemi kasar ta janye daga gasar kasa-da-kasa har na tsawon shekaru biyu, domin gyara matsalolin ta.

Ya kara da cewa shugaban ya kuma nemi a binciki jami'an hukumar kwallon kafa ta kasa domin gano yadda suka kashe kudaden da aka ware musu a lokacin gasar.

Shugaban kungiyar magoya bayan kwallon kafa ta kasar yace babu tabbas ko ta yaya wannan janyewar za ta taimaka wajen samun nasar lashe gasar cin kofin duniya anan gaba.

"Kamata yayi mu kori tsofaffin 'yan wasa, sannan mu kawo sabbin jini, tare da buga wasannin sada zumunta akai-akai," a cewar Olatunde, a hirar sa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Sai dai anasa bangaren Alhaji Ibrahim Galadima, ya gayawa BBC cewa wajibi ne gwamanti ta sauke nauyin da ke kanta.

"Gwamnati ta yi abin da jama'a ke so, ganin irin mummunar rawar da 'yan wasan suka taka, wannan itace bukatar jama'a".

Ya kara da cewa matsalar dai itace ba a san irin tasirin da hakan zai yi ga jama'ar kasar ba wadanda ke da sha'awar kwallon kafa sosai da sosai.

Sai dai a cewar Godwin Dudu-Orumen, mai sharhi kan al'amuran wasanni a Lagos, yana fatan gwamnati za ta sauya matsayin ta, "saboda babbar matsalar kwallon kafa a Najeriya al'amari ne na shugabanci."