Nijeriya da Ghana na rijistar lambobin wayoyin salula

Wasu yan Najeriya na nuna wayoyinsu
Image caption Wasu yan Najeriya na nuna wayoyinsu

A Najeriya, kamfanonin sadarwa na wayar salula na ci gaba da rijistar masu amfani da wayoyin salula a kasar.

Hakan dai ya biyo bayan umurnin da hukumar sadarwa ta Najeriyar ne ta baiwa kamfanonin, na gudanar da rijistar masu amfani da wayar salular, a wani mataki da hukumar ta ce zai rage yawaitar aikata miyagun laifuffuka a kasar.

Haka kazalika a kasar Ghana ma an fara daukar irin wannan matakin, inda daga yau duk wanda ya sayi sabon layin wayar salula, ba zai iya yin amfani da shi ba har sai an yi masa rajista.

A farkon wannan shekarar ce gwamnatin Ghanar ta bullo da sabon tsarin, a wani yunkuri na magance miyagun laifufuka da kuma tabbatar da tsaro a kasar.