Ruwa da iska sun bata gidaje fiye da 400 a jihar Sakkwato

Tasiwirar Najeriya
Image caption Ana jiran agajin hukumomi

A jihar Sakkwaton Najeria, akalla gidaje dari hudu sun lalace – bangayensu suka fadi, iska ya yi sama da rufinsu.

Mutane kuma suna ta faman neman matsuguni da abinci.

Hakan ya biyo bayan iska mai karfin gaske ne da ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a wasu kauyuka hudu jiya.

Shaidu sun ce an kwashe kimanin awoyi biyar iskan na bugawa tare da ruwan saman.

Koda yake babu rahoton an sami hasarar rai, mutanen da suka rasa muhallansu, suna can suna jihan daukin abinci da matsuginni daga wajen hukumomin kananan hukumomi da na jiha.