An samu tsohon shugaban 'yan sandan Afrika ta Kudu da laifin cin hanci da rashawa

Jackie Selebi
Image caption Jackie Selebi

Wata kotu a Afrika ta Kudu ta sami tsohon shugaban 'yan sandan kasar, Jackie Selebi da laifin cin hanci da rashawa.

Ana dai zargin Mr Selebi ne da karbar rashawa ta fiye da dala dubu dari da 50 daga wani mai fataucin miyagun kwayoyi, wanda shi kuma ya nemi a ba shi wasu bayanan sirri daga Hukumar 'yan sanda.

A lokacin da ayke karanta hukuncin alkalin da ya jagoranci shariar, Meyer Hoffe ya ce;"bayan da muka yi nazari a kan dukan shaidun da bangarorin biyu suka gabatar, mun sami wanda ake zargi da laifin cin hanci da rashawa da keta sashe na 4 dokar yaki da cin hanci ta shekara ta 2004".

Mr Selebi dai,wanda har illa yau tsohon shugaban kungiyar 'yan sanda ta duniya, Interpol ne, yana daya daga cikin manyan jami'an 'yan sanda da aka yi wa sharia bisa zargin cin hanci da rashawa a Afrika ta Kudu.