Kungiyar Boko Haram ta ce za ta dau fansa

Malam Muhammad Yusuf, shugaban kungiyar Boko Haram da aka kashe
Image caption Mataimakin shugaban kungiyar Boko Haram ya ce zai dau fansa

A Najeriya, yanzu haka wani faifan bidiyo ya bayyana a Maiduguri wanda ke nuna Malam Abubakar Shekau, mataimakin Malam Muhammad Yusuf, shugaban kungiyar Boko Haram wanda aka kashe.

A faifan bidiyon da ya bayyana, Mataimakin shugaban na kungiyar Boko Haram, wadda aka yi arangama da ita bara, ya jaddada manufar kungiyar, yana mai cewa:

“Boko haramun, democracy ma haramun ne, constitution ma haramun ne”, inji Malam Shekau.

Malam Abubakar Shekau, wanda 'yan sanda ke ikirarin cewa sun kashe shi a watan Yulin bara, yace yana nan da ransa kuma yanzu ya karbi ragamar jagorancin kungiyar.

Ya kuma sha alwashin kai sababbin hare-hare, yana mai cewa sai ya dauki fansar 'yan kungiyar da aka kashe.

“Afka mana aka yi: suka yi harbe-harbe a gun da muke karatu; lallai zan yi jihadi a kan tafarkin Allah da Manzo.

“Sa’annan kuma zan dauki fansar ’yan uwana Musulmai da aka kashe.

“Wannan shi ne kullin da na kulla a zuciya[ta], kuma abin da zan kasance a kai har zuwa mutuwa[ta], ko ni ma in tafi a kan irin hanyar da suka tafi”.

Sai dai 'yan sanda sun yi watsi da ikirarinsa nasa, kana suka ce sun tsaurara matakan tsaro.

Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Borno, Ibrahim Abdu ya shaidawa BBC cewa:

“Wannan zancen banza ne; ta bangarenmu mu ’yan sanda, Muhammadu Yusufu da Abubakar Shekau, wadanda aka yi arangama da su bara, duk an kashesu.

“Shaidanu ne kawai a cikin jama’a suke so su kawo mana tashin hankali.

“Wanda ya kawo wannan bidiyo, a cikin dokar kasa, ya yi laifi; in mun ganshi za mu kama shi”.

Yanzu haka dai kimanin shekara guda ke nan bayan aukuwar rikicin Boko Haram a Jihar Borno da ma wasu jihohin arewacin Najeriya, al’amarin da ya haddasa mutuwar mutane da dama.