FIFA ta gargadi Najeriya

Najeriya ta sha kashi a gasar ta bana
Image caption Najeriya ta sha kashi a gasar ta bana, inda ta zamo ta karshe a rukunin B

Hukumar kwallon kafa ta FIFa ta umarci Najeriya da ta soke dakatarwar data yiwa kungiyar kwallon kafa ta kasar daga gasar kasa-da-kasa har na tsawon shekaru biyu daga nan zuwa ranar Litinin. Hukumar FIFA tace idan har ba a janye dakatarwar ba to za ta dakatar da Najeriya daga dukkan harkokin kwallon kafa.

Mai magana da yawun hukumar ta FIFA Nicolas Maingot ya gayawa manema labarai cewa: "FIFA ta aikawa da Najeriya wasika, inda ta bata wa'adin zuwa karfe shida na ranar Litinin ta janye matakin data dauka na hana kasar buga wasannin kasa-da-kasa har na shekaru biyu."

"Rashin yin hakan zai sa a dakatar da hukumar kwallon kafa ta kasar wato NFF, kuma FIFA ba za tayi aiki da kwamitin rikon da gwamnatin Najeriya ta kafa ba."

A ranar Laraba ne Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya dakatar da kungiyar ta Super Eagles sakamakon mummunar rawar da ta taka a gasar cin kofin duniyar da ake yi a Afrika ta Kudu.

Gwamantin tace ta yi hakan ne domin samun damar gyara harkokin kwallon kafa a kasar wadanda suke ci gaba da tabarbarewa.

Hukumar ta FIFA za kuma ta tura dan kwamitin ta na zartarwa Dakta Amos Adamu, wanda dan Najeriya ne zuwa kasar domin kokarin shawo kan lamarin.

Hukuncin da Najeriya za ta fuskanta zai hada da dakatar da kasar da kuma klob klob da alkalan wasa na kasar daga wasannin da FIFA da CAF ke shiryawa, tare da dakatar da baiwa kasar kudaden shiga na FIFA da CAF.

Mista Maingot ya kara da cewa: " Wannan matakin zai hada da dakatar da baiwa kasar dukkan wani tallafi na hukumar ta FIFA, tare da hana jami'anta halartar dukkan wata gasa."