'Yan gundun hijrar Somalia zuwa Kenya na raguwa

Somalia
Image caption Somalia

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yawan 'yan gudun hijirar Somalia dake zuwa Kenya da Yemen, ya ragu sosai tun farko wannan shekarar.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya , UNHCR ta ce raguwar da aka samu ba tana nufin an samu kwanciyar hankali a Somalia ba ne, illa dai jamaa da dama da ke neman ficewa daga kasar suna gamuwa da cikas ne saboda rashin abubuwan sufuri da kuma wuraren bincike da dakarun sa kai ke kafawa.

Daruruwan dubban 'yan Somalia ne dai suka nemi mafaka a kasashe makwabta a cikin shekaru 20 da aka shafe ana yakin basasar kasar.