Hukumar abinci ta duniya ta bukaci taimakon abinci ga Nijar

Tambarin hukumar abinci ta duniya
Image caption Tambarin hukumar abinci ta duniya

A jamhuriyar Nijar hukumar agaji da abinci ta duniya -WFP ( PAM ) ta yi kira ga kasashe da kungiyoyi na duniya su agaza wa kasar Nijar.

Hukumar na neman taimakon ne domin shawo kan matsalar tamowar da ke addabar yara yan kasa ga shekaru 5 da haihuwa.

Kungiyar ta ce al'amarin tamowar ya yi kamari a kasar ta nijar.

Binciken da kungiyar ta yi ne daga ranar 24 ga watan mayu zuwa 15 ga watan yuni na shekara ta 2010 ya tabbatar da kashi 16,7 cikin 100 na yaran ke cikin matsatsi.