Brazil zata karfafa hulda da Afrika

Shugaban Brazil
Image caption Shugaban Brazil

Shugaban Brazil, Luiz Inacio Lula da Silva ya fadawa taron shugabannin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da ake yi a tsibirin Cape Verde cewa Brazil ta kuduri anniyar karfafa huldarta da Africa.

Shugaba Lula, wanda ke ziyarsa ta karshe a Afrika kafin ya sauka daga kan mukaminsa a karshen shekara, ya ce akwai wani nauyi na Afrika mai cike da tarihi, wanda Brazil ba za ta iya saka ma ta ba.

Sai dai ya ce wanda zai gaje shi na da hakkin ya karfafa huldar kasuwanci da Afrika da batun saka jari a Afrika da kuma musayar fasaha.

Wakilin BBC ya ce shugaba Lula ya fifita batun karfafa hulda da Afrika a manufarsa ta harkokin waje, kuma a tsawon shekaru 8 din da ya shafe a kan karagar mulki, darajar cinikayya tsakanin Brazil da Afrika ta rubanya har sau hudu.