Mutane dari biyu sun mutu a Congo

Congo
Image caption Congo

Akalla mutane dari biyu sun rasa rayukansu, sakamakon bindigar da wata tankar mai ta yi a Gabashin Jamhuriyar Dimukradiyyar Congo.

Wani kakakin Ofishin Majallisar Dinkin Duniya a kasar, Madnodje Mounoubai ya ce sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniyar dake Congon da sauran kungiyoyi na taimakawa wajen kai dauki ga wadanda suka samu raunika:

Ya ce a halin yanzu, muna kokarin kwashe wadanda suka samu raunika ne zuwa asbitin da ya fi kusanci.

A karfe tara na safiyar yau, an yi nasarar kai kusan mutane 35 zuwa asibitin garin Bukavu.

Tankar ta juye ne, kusa da kauyen Sange a jiya da daddare, sannan ta yi bindiga yayinda jama'a ke kokarin dibar man dake tisyaya daga tankar a cikin duhu.

Sojojin Congo da dama ne dai ke zaune tare da iyalansu a kauyen na Sange, wanda ke kusa da iyakar Burundi.