Iran zata rubanya kayayyakin da take fitarwa waje

Mahmoud Ahmadinejad
Image caption Mahmoud Ahmadinejad

Shugaban Iran, Mahmoud Ahmadinejad, ya ce yawan kayyakin da Iran za ta fitar waje zai ribanya har sau uku, duk kuwa da sabbin takunkumin da Amruka ta saka wa kasar.

A ranar Alhamis data wuce ne dai shugaba Obama ya sa hannu a wasu jerin matakai da nufin karya lagon Iran din game da shirinta na nukiliya.

Sai da shugaba Ahmadinejad ya ce kasashen Yammacin duniya su kuka da kansu.

Ya ce shekaru hudu da suka wuce, sun kakabawa Iran takunkumi a lokacin da darajar kayyakin da take fitarwa take dala biliyan shida a shekara.

Amma yanzu yakai dala biliyan 18, kuma za ta karu zuwa dala biliyan 60 nan da shekaru uku.