Pentagon ta tsaurara alaka da 'yan jarida

Sakataren tsaron Amurka Robert Gates
Image caption Ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta ce duk wani jmi'in soja sai ya sanar da magabatansa kafin ya yi hira da 'yan jarida

Sakataren tsaron Amurka, Robert Gates, ya bayar da umurnin a tsaurara huldar dakarun kasar da kafofin yada labarai.

Wannan mataki dai na zuwa ne 'yan kwanaki bayan Shugaba Obama ya sallami babban kwamandan dakarun kasar a Afghanistan, Janar Stanley McChrystal, saboda wasu kalamai da ya yi na sukar wadansu manyan jami'an gwamnati a wata hira da mujallar Rolling Stone.

A wata wasika da ya aike mai shafi uku, Mista Gates ya nuna damuwa a kan yadda aka samu sakaci a huldar soja da 'yan jarida.

Ya kuma bayar da umurnin cewa nan gaba, duk wani babban jami'in soja sai ya sanar da magabatansa kafin ya yi hira da wata kafar yada labarai.

Sai dai wani mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Pentagon ya musanta cewa wannan matakin na da alaka da hirar da Janar McChrystal din ya yi da wani dan jarida.