Gubar dalma: Zamfara ta ce ba a gargade ta ba

Wani wurin da ake hakar zinare
Image caption Mutane da dama sun mutu sakamakon mu'amala da gubar dalma ta hanyar hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba

A Najeriya, wata takaddama ta barke tsakanin ma'aikatar kula da hakar ma'adinai ta kasar da kuma gwamnatin Jihar Zamfara, bayan ma'aikatar ta ce ta ankarar da hukumomin jihar dangane da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

A wani rahoto da ta fitar, ma’aikatar ta ce ta aikewa hukumomin jihar wasikun gargadi har guda goma dangane da hakar ma'adinai tsakanin 2007 zuwa 2009—shekaru kafin mutuwar mutane fiye da dari da sittin sakamakon mu'amala da sinadarin dalma a jihar.

Rahoton ya kuma ce daga cikin wadanda aka aikewa wasikun gargadin har da gwamnan jihar, Alhaji Mahmuda Aliyu Shinkafi, wanda ma’aikatar ta ce ta aikawa wasika ranar 23 ga watan Yunin 2008.

Gwamnatin jihar dai ta musanta samun wani gargadi daga ma'aikatar ta tarayya.

Kwamishinan yada labarai na jihar ta Zamfara, Aliyu Adamu Tsafe, ya ce kamata ya yi a kyale gwamnatin jihar ta ji da “juyayin abin da ya same mu” na asarar da mu’amala da sinadarin dalma ta haifar, a maimakon a taso da irin wadannan maganganun.

“Me ya sa tuntuni ba a fito da maganar ba sai yanzu?

“Ni ina ganin ma siyasa ce ta shigo yanzu: kila ana so a hada gwamnatin Zamfara da gwamnatin tarayya [ne] shi ya sa aka kawo wannan labarin a halin yanzu”, inji kwamishinan.

Ita ma dai Majalisar Dattawan Najeriya ta tafka muhawara dangane da wannan al’amari na gubar dalma, wadda ta yi sanadiyyar asarar rayukan mutane masu yawa a wasu kauyuka biyar na Jihar Zamfara.

Majalisar ta tafka muhawarar ne a kan wani kuduri wanda zai duba ayyukan kamfanonin da ke siyan ma'adinai daga hannun masu hako shi, da batun diyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma takaita aikin hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba.

Sanata Sahabi Ya'u, wanda ya gabatar da kudurin ga Majalisar Dattawan, ya ce ya gabatar da kudurin ne don “mu nunawa Najeriya da mutanen duniya baki daya cewa muna bukatar a yi mana jaje bisa ga abin da auku ga jama’armu; sannan mu zakulo abin da muke sa ran cewa shi ne babban dalilin da ya sa wadannan abubuwa suke aukuwa”.

Dan majalisar ya ci da cewa: “Babban abin da muke tunani shi ne daya daga cikin illolin shi ne yadda gwamnatin tarayya ke bayar da lasisin hako ma’adinai ba tare da jihohi sun san wadanda aka ba ko yadda aka bayar ba.

“[Mun kuma] nemi a ba jihar da su al’ummar da abin ya shafa tallafi, domin abin yana son ya fi karfin jiha....”

Ya kuma ce an bukaci wadansu kwamitoci na Majalisar Dattawan su binciko irin rawar da wadanda ke sayen ma’adinan ke takawa a wannan al’amari don a dauki mataki a kansu.