Janar David Petraeus zai fara aiki yau

Sabon Kwamandan dakarun kasashen duniya a Afghanistan David Petraeus
Image caption Sabon Kwamandan dakarun kasashen duniya a Afghanistan David Petraeus zai kama aikinsa yau

A yau ne sabon kwamandan dakarun kasashen duniya a Afghanistan zai fara aiki.

Janar David Petraeus na karbar ragamar aiki ne daidai lokacinda mayakan Taliban ke kara hare-haren da suke kaiwa dakarunsa.

Watan Yulin da mu ke ciki, shi ne wanda aka fi asarar sojoji tun bayan mamaye kasar shekaru tara da su ka wuce, inda 'yan Taliban su ka kashe fiye da soji dari daga farkon watan.

An ambato Janar Petraeus yana cewar aiki ne mai wuya, kuma babu wani sauki a tattare da shi, amma yace 'idan mu ka hada kai za mu yi nasarar cimma manufarmu'.

An dai kori kwamandan da ya gada ne Stanley McCrystal, a farkon watan nan bayanda ya soki gwamnatin shugaba Obama.