Ana juyayin rasuwar Ayatullah Fadlallah a Lebanon

Ayatullah Fadlallah
Image caption Ayatullah Fadlallah

Ana ta nuna juyayi da alhini a Lebanon da sauran kasashen Musulmai, sakamakon mutuwar daya daga cikin manyan malaman Shi'a da suka fi karfin fada a ji, Ayatullah Mohammed Hussein Fadlallah.

Ya rasu ne yau a wani asbiti na birnin Beirut, yana da shekaru 74. Magoya bayansa sun yi kiran zaman makoki na kwanaki 3, kuma zaa yi jana'izarsa ranar Talata.

Jakadan Iran a Lebanon, Ghadanfar Roken Abadi yana daga cikin wadanda suka mika ta'aziyarsu.

Jakadan Ya ce a madadin jagoran addinin Iran, Ayatullah Sayyed Ali Khamenei da shugaban kasa, Mahmoud Ahmadinejad da kuma al'ummar Iran, ina mika ta'azziya bisa awnnan babban rashi da mu ka yi. Ayatullah Mohammed Hussein Fadlallah dai ya samu dimbin magoya baya a Lebanon da Iraqi da kuma yankin baki daya saboda tarbiyar da yake ba mutane.