An fasa bututun dake kai mai Turkiyya daga Iraki

Bututun mai
Image caption Bututun mai

An fasa wani bututu dake kai man fetur daga Iraki zuwa Turkiyya.

Harin, wanda aka kai a jiya da yamma, kusa da garin Midyat na kudu maso Gabashin Turkiyya, ya haddasa tashin gobara, wadda sai yau da asubahi ne aka shawo kanta.

Bututun dai ya taso ne daga birnin Kirkuk na Arewacin Iraki zuwa tashar jiragen ruwan Jeyhan dake gabar tekun Mediteraniya.

Kawo yanzu babu kungiyar da ta ce ita ke da alhakin kai harin, amma ana kyautata zaton aikin Kurdawa masu fafitika ne na kungiyar PKK.

A baya dai sun kai kai hari a kan bututun.