Hillary Clinton tana ziyara a Azerbaijan

Sakatariyar hulda da kasashen wajen Amurka Hillary Clinton
Image caption Sakatariyar hulda da kasashen wajen Amurka Hillary Clinton na ziyara a Azerbaijan

Sakatariyar hulda da kasashen waje ta Amurka Hillary Clinton na Azerbaijan, a ziyarar da ta ke yi a kasashen Gabashin Turai guda biyar bayanda ta ziyarci Ukraine da Poland.

Ana sa ran tattaunawarsu da shugaban kasar Azerbaijan, Ilham Aliyev za ta maida hankali ne kan rikicin yankin Nagorno Karabakh-inda Armeniyawa su ka fi yawa.

Amurkan dai ita ce mai sasanta tsakanin Azerbaijan da Armenia dangane da yankin, amma kawo yanzu ba ta kai ga cimma nasara ba.

A ranar Litinin ne Mrs. Clinton za ta karasa Armenia sannan ta kammala ziyarar ta ta a Georgia.