An fidda jadawalin zabubbuka a Nijar

Shugaban mulkin sojin Nijar Salo Djibo
Image caption Hukumar zaben kasar Nijar ta fidda jadawalin zabubbukan da za'a gudanar a badi

A jamhuriyar Nijar hukumar zabe mai cikakken 'yanci, CENI ta bayyana jadawalin zabubbukan da za ta shirya a kasar.

Hukumar zaben, CENI ta kuma ce tana bukatar SEFA biliyan 30 domin gudanar da zabubbukan.

A jiya ne dai shugaban hukumar Malam Ghusman Abdraman ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai da ya kira a Yamai.

A farkon badi ne za'a gudanar da zabubbukan da za su mai da jamhuriyar Nijar ga mulkin farar hula.

Shugaban hukumar zabe ta Nijar, Abdurraman Gusman ya baiyana cewa a watan Janairu za'a yi zaben shugaban kasa amma sai watan Maris za'a kammala bayyana sakamako.

Tun watan Fabrairu ne dai sojoji ke mulkin Nijar bayanda su ka hambarar da gwamanatin shugaba Tandja Mammadou, bayan da ya sauya tsarin mulkin kasar don baiwa kansa damar yin tazarce.