Yau ake zaben shugabankasa a Poland

Zaben shugabankasa a kasar Poland
Image caption A yau al'ummar kasar Poland ke zaben shugabankasarsu bayan mutuwar tsohon shugabankasar a wani hatsarin jirgin sama

A yau ne al'umar Poland ke kada kuri'ar zaben shugaban kasar da zai maye gurbin Lekh Kacinski da ya rasu a hatsarin jirgin sama a watan Afrilu.

Dan uwan tagwaitakar marigayin, Yaroswav Kacinski, mai ra'ayin gurguzu ne ke takara da Broniswav Komoroski na jam'iyyar Civic Platform mai mulkin kasar, wacce ke da ra'ayin 'yan jari hujja.

Mr. Komorowski ne ya samu kuri'u mafi yawa a zagayen farko na zaben amma kuri'un jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan na nuna cewa yanzu kan-kan-kan su ke da abokin takararsa.

A mafi yawan lokuta dai shugaban kasar Poland na da matsayi ne na jeka-na-yi-ka, sai dai ya na da ikon hawa kujerar na ki kan kudirorin majalisar dokokin kasar.