Iran ta zargi Amruka da sace masanin kimiyyar kasarta

Mr Amiri
Image caption Mr Amiri

Iran ta ce tana da hujjojin dake nuna cewa kungiyar leken asirin Amruka ta sace daya daga cikin masana kimiyar kasar a bara.

Ma'aikatar harkokin wajen Iran din ta ce ta mika wasu takardu dake da alaka da masanin kimiyar nukiliya, Shahram Amiri, ga Ofishin jakadancin Switzerland, wadda ke wakiltar Amruka a kasar ta Iran.

Gwamnatin Iran dai ta ce za ta yi duk abun da za ta iya don kare 'yan kasar ta.

Wakilin BBC ya ce an yi ammnar cewa Shahram Amiri ya yi sama ko kasa ne a lokacin da yake gudanar da aikin Hajji a Saudiyya a bara, kuma iyalansa sun ce tun waccan lokaci, ba su ji duriyarsa ba.