Ana gudanar da zabe a Mexico

Mexico
Image caption Mexico

Ana gudanar da zabe a rabin jihohin kasar Mexico cikin tsauraran matakan tsaro, bayan da aka yi fama da kashe-kashe da kuma barazanar aikata kisa daga kungiyoyin masu fataucin miyagun kwayoyi.

Wakilin BBC ya ce 'yan watanni gabannin zaben, 'yan takara a wasu jihohin na Mexico sun koka cewa masu fataucin miyagun kwayoyi na yin barazana ga rayuwarsu.

Jama'a na zabar sababbin wadanda zasu rike mukamin magajin gari da kuma gwamnoni ne, amma galibi hankalin su ya tashi ainun saboda tashin hankalin da aka yi fama da shi.

An dai bindige 'yan takara biyu har lahira, tare da yin ruwan bam a kan Hedkwatocin yakin neman zabensu a Arewacin kasar ta Mexico.

Hakazalika rahotanni sun ce daruruwan jami'an zabe sun yi murabis a jiha daya, bayan da masu aikata miyagun laifufuka suka yi barazana ga rayuwarsu.