Wasu jam'iyyun adawa a Nijar sunyi maraba da jadawalin zabe

Shugaban mulkin sojin Nijar Salou Djibo
Image caption Jam'iyyar PNDS Tarayya, madugar adawa a Nijar ta bayyana gamsuwarta game da tsare tsaren zaben badi

A jamhuriyar Niger wasu jamiyyun siyasar kasar sun fara tofa albarkacin bakinsu game da zaben shugaban kasar da za'a yi ranar uku ga watan daya na badi kamar yadda hukumar zabe, ta CENI ta baiyana. Jam'iyyar PNDS TARAYYA madugar adawar Niger, ta yi marhabin da wannan tsari da zai kawo karshen kasancewar sojoji a kan madafun iko a Niger tun bayan kawarda gwamnatin malam Mamoudu Tandja da sojojin suka yi a ranar 18 ga watan biyu na bana.

Mataimakin shugaban jamiyyar PNDS -TARAYYA Malam Bazoum Mohammed ya shaida wa BBC cewar sun gamsu da yadda hukumar zaben kasar take gudanar da ayyukanta

Ya kuma ce zasu fuskanci wannan zabe ba tare da kowacce irin fargaba ba