Ejup Ganic zai bayyana a gaban kotu yau

Tsohon Shugaban Bosnia Ejup Ganic
Image caption Tsohon Shugaban Bosnia Ejup Ganic zai fuskanci shari'a a yau, bayan da Serbia ta zarge shi da aikata laifukan yaki a shekarar 1992

Tsohon shugaban Bosnia Ejup Ganic zai bayyana a gaban wata kotun majistire a yau domin fara shariar zargin gwamantin Serbia take masa.

Serbia tace Ganic yana da hannu a aikata laifukan yaki a shekarar 1992, zargin daya musanta.

An tsare Ejup Ganic a filin jirgin saman Hethrow a farkon watan Maris bayan daya kai wata ziyara takaiatacciya zuwa burtaniya.

'Yan sanda ne suka tsare shi bayan da serbia ta basu umarnin yain hakan. sabiyan dai tayi zargin cewar a shekarar 1992 lokacin da aka fara yakin Bosnia, Ejup Ganic ya bada umarnin a kashe sojojin sabiyan dake gujewa birnin Sarayebo.