Interpol ta bukaci jama'a su bayyana mata wadanda ake nema ta Intanet

Interpol
Image caption Interpol

Hukumar 'yan sanda ta Duniya -Interpol ta bukaci Jama'a a cikin duniya da su bayar da rahoton ganin mutanen da take nema ruwa a jallo wadanda kuma ta rasa inda suka shige, idan sun gansu a cikin shafukan internet na mu'amalar jama'a kamar irinsu Facebook.

Hukumar 'yansandan duniyar ta fitar da hotunan mutane 26 da take nema -- wadanda suka hada da wadanda ake zargi da kisan kai da fataucin mutane da kuma masu lalata da kananan yara.

Shugaban sashen ayyuka na hukumar ya ce, mai yiwuwa a fi ganin mutanen a ire iren wadannan shafuka fiye da a kan tituna.

Wakilin BBC ya ce hukumar ta 'yansandan duniya ta ce ta hari mutane 450 da suka guji shara'a tun cikin watan Mayu, kuma tuni imma dai an kama ko kuma an san inda fiye da dari daya suke.