Jam'iyyar dake mulki ita ce ke kan gaba a Poland

Zaben shugabankasa a kasar Poland
Image caption A yayinda ake saran bayyana sakamakon zaben kasar Poland a yau, alkaluma na nuna cewarJam'iyyar dake mulki ita ke kan gaba

A yau ne za'a baiyana sakamakon zaben shugaban kasar Poland bayanda tuni alkalumma ke nuna cewa shugaba mai ci ne ya yi nasara.

Ayayinda aka kidaya kusan dukkan kuri'un da aka kada a zaben shugaban kasar Poland, dan takarar jam'iyyar da ke mulki na cigaba da baiwa abokin karawarsa tazara.

Alkaluman baya-bayan nan sun baiwa Broniswav Komorowski kaso hamsin da uku na kuri'un yayinda Yaroswav Kachinski ke da kaso arba'in da bakwai.

Sai dai Mr. Komorowski ya bukaci magoya bayansa kada su yi riga malam masallacin taya shi murna kafin baiyana zaben a hukumance a yau Litinin.