Yaki da sace sacen mutane a kudu maso gabacin Najeriya

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan
Image caption Gwamanonin jahohin kudu maso gabacin Najeriya zasu fara amfani da tsauraran matakai wajen yaki da sace sacen mutane da kuma garkuwa dasu

A Najeriya, gwamnonin jihohi biyar na shiyyar kudu maso gabashin kasar, sun yanke shawarar bin tsauraran matakai, domin shawo kan matsalar yawan sace mutane da kuma garkuwa da su har sai an bayar da makudan kudi kafin a sako su.

Gwamnonin sun yi barazanar tube duk wani basaraken gargajiya da ya yi sake aka sace wani a yankin masarautarsa.

Gwamnonin sun yanke shawarar ce, a wani taro da suka gudanar a birnin Enugu a daren jiya.

Sace sacen mutane da kuma garkuwa dasu domin neman kudin fansa wata matsala ce dake cigaba da ciwa hukumomin najeriya tuwo a kwarya