China zata gina matatun mai na biliyoyin daloli a Najeriya

China ta ce za ta gina wata matatar mai ta dala biliyan 8 a Lagos, babban birnin kasuwancin Najeriya.

Yarjajeniyar tare da wani kamfanin ayyukan injiniya na gwamnatin China, watau CSCEC, wani bangare ne na wata yarjejeniyar da ta zarta dala biliyan 20, wadda kuma ta hada da wasu matatun man guda biyu.

A wani lamarin na dabam kuma, katafaren kamfanin tarho na India, Bharti Airtel, ya ce zai saka dala miliyan 600 a kasuwar wayar salula ta Najeriya nan da shekara guda.

A farkon wannan shekarar ce Bharti Airtel ya sayi Zain, wanda wani babban kamfanin sadarwa ne a Afrika.